Harkokin zabe musamman a Kasashe masu tasowa irin Najeriya al'amari ne da aka shafe tsawon lokaci ana fadakar da alumma a kai, da su nisanta kansu daga ‘yan siyasa marasa kishin kasa da ke amfani da damar wajen sayen kuri’un jama’a a lokutan zabe, daga karshe a zo ana da an sani.
A hirar ta da Muryar Amurka, Sanata Patricia Naomi Akwashiki, daya daga cikin shugabannin jam’iyyar ADC kuma ganau da ta shaida yadda al’amura suka wakana a zaben jihar Ekiti, ta ce wannan abu bai zama abun damuwa ba, amma lokacin da aka fara amfani da BVAS ana zabe, taga ana sayan kuri’a a zaben gwamna da suka je jihar Ekiti, inda wasu jam’iyyu ke sayan kuri’a a kan N10,000 ko N5,000 ko N3,000. Ta ce su da ke kananan jam'iyyu ba su san makomarsu ba.
Talauci ya kasance daya daga cikin matsalolin da ke sanya jam’iyyun siyasa yin amfani da kudi wajen sayan kuri'u na al’umma, abinda ya sa akasari ba cancanta ake bi ba, lamarin da Kabiru Hussaini shugaban jamiyyar ADC ta jihar Jigawa ya ce illar hakan kuwa zai gurbatar da ci gaban da ake yekuwar samu a Najeriya.
A nashi bayanin, dan takarar kujerar Sanata daga jihar Gombe, Ahmad Adamu, ya ce mutanen Najeriya a yanzu ba za su gayawa duk wata kasa a duniya irin wahalar da suka sha ba, su suka fi kowa sanin wahalar da suka sha, idan suna ganin ba za su iya yiwa kansu kiyamar laili ba a kan wannan matsala a, su samarwa kan su ‘yanci, da samu saukin rayuwa. Ya ce ai dukkansu sun wahala, amma yana da yakinin mutane sun yi korafi sun wahala kuma su za su canza da kan su za su zabu cacanta.
A nata bangaren dai hukumar zabe ta INEC ta ce tana aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an bi ka’idojin zabe a kasar kuma sun jadadda batun hukunta duk wani dan siyasa da aka kama da laifin amfani da kudi wajen jan hankalin talakawa masu jefa kuri’a a ranakun zabe na shekarar 2023.
Jami’ar yada labarai a hukumar ta INEC Zainab Aminu ta yi kira ga masu kada kuri’u da su yi amfani da cancanta wajen zaben mutanen da za su yi musu aiki ba tare da la’akari da masu basu kudi ba.
Ana dai fatan zaben shekarar bana ya banbanta da na shekarun baya, domin samun shugabannin masu kishin kasa da zasu taka rawar gani wajen samawa kasar mafita daga matsalolin da ke addabarta.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim: