Wani kwamiti mai mutane bakwai da shirin ba matasa lamuni domin dogaro da kai ya fara gudanar da ayyukan tantance mutane dubu arba'in 40,000 da suka cika takardar neman bashi a karkashin shirin nan na bada rancen kudi Naira biliyan 10 domin baiwa matasa da ke shi'awar shiga harkokin kasuwaci na Bank of Industry .
Mujallar Vanguard ta wallafa cewa shirin ya kara yawan mutanen da zasu ci moriyar wannan shiri na rance domin kafa jari daga mutane dubu daya da dari biyu (1200) zuwa dubu hudu (4000) a kowace shekara, kuma kowannen su zai sami rancen kudi har na zun zurutun kudi Naira miliyan Biyar (5000,000).
Ana kuma sa ran cewa shirin ba matasa rancen jari domin gudanar da sana'o'in dogaro da kai zai sama wa matasan Najeriya maza da mata guraben ayyuka guda dubu talatin da shidda (36,000).
Shirin bada lamunin yazo daidai ne da sabon kudirin gwamnatin taraiyya na samar wa matasa maza da mata kama daga shekaru goma sha takwas zuwa talatin da biyar da haihuwa (18 - 35)guraben ayyukan yi.