Kwamitin Lambar Yabo na Abinci ya karrama tsoffin Shugabannin kasashen Ghana da Brazil

  • Ibrahim Garba

Tsoffin Shugabannin Ghana da Brazil

Sakamakon baya bayan nan na zaben Shugaban Kasar Liberiya

Sakamakon baya bayan nan na zaben Shugaban Kasar Liberiya ya nuna cewa Shugaba mai ci Ellen Johnson Sirleaf na kan gaba, to amman ta kasa samin adadin kuri’un da zai sa ta kauce wa zagaye na biyu na zaben.

Sakamakon wuccin gadin da hukumar zaben Liberiya ta bayar a jiya Alhamis ya nuna Mrs Sirleaf na da kimanin 44% na kuri’un. Na biye da ita, Mr. Winston Tubman, na da kimanin 26%.

Sakamakon ya nuna cewa tsohon shugaban ‘yan tawaye Sanata Prince Johnson na matsayi na 3 inda ya sami 13%.

Sai dan takara ya sami 50% kafin a ce ya ci. Idan ya zama dole, to za a gudanar da zaben fidda gwanin ne ran 8 ga watan Nuwamba. Wakilin Muryar Amurka a Liberiya, James Butty, y ace da yawa na ganin duk wanda Johnson ya mara wa baya daga cikin ‘yan takara biyu masu tsayawa zaben fidda gwanin ne zai ci ko za ta ci.