Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce gwamnatin shi, ta na duba yiwuwar yin amfani da duk wata damar da ta ke da ita, bayan makarkashiyar neman yin kisan gilla ga jakadan kasar Saudiyya a nan Amurka.
Mr.Obama ya yi wannan furuci ne a yayin wani taron manema labarai tare da shugaban kasar Kuriya ta Kudu Lee Myung-bak a nan birnin Washington DC.
Ya ce a bayyane ya ke, akwai wadanda su ka san da wannan makarkashiya a cikin gwamnatin kasar Iran, kuma ya ce wannan wani take-take ne mai hatsari da ganganci.
Haka kuma Mr.Obama ya ce gwamnatin kasar Iran ta dade ta na sabawa ka’idar kasa da kasa, sannan ya ce zai tabbatar da cewa Iran ta dandana kudar ta saboda irin wannan halayya na ta.
Shugaban na Amurka ya ce matakin farko shi ne mikawa shari’a wadanda ke da hannu a ciki. Har wa yau kuma ya ce Amurka za ta dauki matakan ladabtarwa mafiya gauni, domin ta kara maida gwamnatin kasar Iran saniyar ware.