Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Ce Ya Gama Jiran 'Yan Majalisar Dokoki Akan Maganar Ayyukan Yi


Shugaban kasar Amurka Barack Obama a lokacin da ya ke ganawa a yau talata da kwamitin shi na farfado da tattalin arziki a Pittsburgh, jahar Pennsylvania.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama a lokacin da ya ke ganawa a yau talata da kwamitin shi na farfado da tattalin arziki a Pittsburgh, jahar Pennsylvania.

Shugaban Amurka Barack Obama Ya ce shikenan ya gama zaman jiran 'yan majalisar dokoki

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce shikenan ya daina jiran ‘yan majalisar dokoki su yi wani abun zaburar da tattalin arzikin kasar.

Shugaban ya fada a wurin wani taron kwamitin shi na farfado da tattalin arziki a yau talata a Pittsburgh, jahar Pennsylvania cewa al’ummar Amurka ba za ta iya ci gaba da jira ba. Ya ce tuni dai ma’aikatan shi, su na aiki kan hanyoyin habaka tattalin arziki da kirkiro ayyukan yi ba tare da an bukaci dokar amincewa yin hakan ba.

Mr.Obama ya gana da kwamitin wanda ya kunshi shugabannin kamfanoni da na kwadago domin sake duba rahoton da kwamitin ya gabatar a baya-bayan nan akan hanyoyin kirkiro ayyukan yi da karfafa tattalin arziki. Rahoto ya bukaci a kara kashe kudi a kan muhimman abubuwan kyautatawa jama’a da kuma rage matsanantan ka’idoji, da haraji da gyaran dokar shigi da fici.

Sun yi wannan ganawa ce a daidai lokacin da Mr. Obama ke ci gaba da yin matsin lambar amincewa da shirin shi na dola miliyan dubu 447 na samar da ayyukan yi a Amurka, wanda majalisar dattabai za ta yi kuri’ar farko a kai a yau Talata.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG