Kasa da mako biyu kafin a fara babban zabe a Najeriya, wani malamin jami'ar Jos, ya yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da jam'iyun siyasa, su himmatu wajen fadakar da jama'a kan yadda za su kaucewa abubuawa da za su lalata musu kuri'u.
Vincent James Dawap, ya yabawa hukumar zabe wajen tafiyar da ayyukanta, ya na mai cewa jama'a sun waye game da muhimmancin siyasa.
Daga nan ya kuma kira ga jam'iyun siyasa cewa su dage wajen fadakarwa.
Mr. Vincent ya ba da shawarar a kaucewa daukar matasa wadanda suke cikin halin maye a matsayin jami'an siyasa ko wakilansu a rumfunan zabe, domin a cewarsa wadan nan ne suke janyo fitina a lokutan zabe.
Shugaban wata kungiyar tallafawa jama'a ta matasa, Ibrahim Farouk, ya ce akwai muhimmiyar taimako da kafofin yada labarai za su iya bayarwa wajen ilmantarda jama'a kan yadda za su dangwala yatsa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5