Kuri'ar Gayyatar Shaidu Ta Yau Asabar Ka Iya Tsawaita Shari'ar Tsige Trump

Shari'ar tsigeTrump

Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri’ar bada sammacin gayyato shaidu su bada bahasi a wannan shari’ar tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump.

‘Yan Republican biyar sun kada kuri’a tare da ‘yan Democrat 50 a majalisar dattawan na neman jin bahasi daga shaidu. Sai dai sakamakon wannan kuri’ar ya zo da al’ajabi, yayin da ake sa ran majalisar dattawa zata kammala jin mahawara daga bangarorin kana tana iya daga bisani ta kada kuri’ar wanke Trump ko kuma hukunta shi, matakin da zai kawo karshen shari’ar da aka fara a ranar Talata.

Matakin kira shaidun na nufi da shari’ar zata ci gaba har izuwa akalla mako mai kamawa.

Dan majalisar wakilai Jamie Raskin dake jagorantar masu shigar da karar daga majalisar wakilai, ya sanar cewa yana so ya gayyaci ‘yar majalisar wakilai ta Republican Jaime Herrera Beutler mai wakiltan jihar Washington.

Beutler ta fitar da wata sanarwa da yammacin ranar Juma’a cewa, shugaban marasa rinjayi a majalisar wakilai Kevin McCarthy ya fada mata cewa Trump ya nuna goyon bayan sa ga masu tarzomar a wata zazzafar hirar waya tsakanin su biyun game da hari kan majalisar dokoki. McCarthy ya kira Trump ne domin ya yiwa masu tarzomar magana da su daina tashin hankalin.

Da safiyar yau Asabar, kafafen yada labaran Amurka da dama, sun ambaci wata majiya da ta nemi a sakayata tana mai cewa shugaban marasa rinjayi a majalisar dattawa dan Republican Mitch McConnell ya fadawa ‘yan jami’aiyarsa a majalisar cewa zai kada kuri’ar wanke tsohon shugaban a yau Asabar.

A ranar Juma’a, lauyoyin Trump sun kammala bayanan kariya da suke baiwa tsohon shugaban na Amurka, inda suka musanta cewa ya ingiza taron jama’a su kai mummunar hari a kan majalisar dokoki a ranar shida ga watan Janairu. Lauyoyin Trump sun kwatanta wannan shari’a da wani bita da kullin siyasa ce kawai.

Lauyoyin Trump sun bada bahasin su ne a cikin sa’o’I uku a ranar Juma’a, amma basu yi amfani da sa’o’I 16 da aka basu su gabatar da bayanan su.