Kurdawan Syria Na Barazanar Fara Yakin Sari Ka Noke A Afrin

Mayakan 'yan tawayen Syria dake samun goyon bayan Turkiya

Kurdawan Syria suna barazanar kara kaimi a yakin sari ka noke, bayan da sojojin Turkiya da kawayensu a Syria, suka karbe ikon kan garin Afrin, dake arewacin Syria, wanda tungar Kurdawa ne.


Wani babban jami’in Kurdawan Othman Sheikh Issa yace, dakarunsu zasu ci gaba da hana dakarun Turkiyya sakat a garin. Yace dakarun su zasu kai hare hare a kan Turkawa abokan gaba da kawayen su sojojin-haya a duk sukuni da suka samu.
Sojojin Turkiya da kawayen su na Syrian sun kafa tuta a tsakiyar Afrin a jiya Lahadi, suka ayyana samun cikakken ikon yankin bayan da basu huskanci turjiya daga mayakan sakai na kurdawan ba da ake kira People’s Defense Units, ko PDU a takaice.
Turkiya tana kallon YPG a matsayin bangare na kungiyar ma’aikatan Kurdawa ko PKK a takaice, kungiyar sari ka noken nan da take yaki kafa kasar kurdawa da zata kunshi wani Turkiyya.
Turkiya ta ayyana PKK a zaman haramtacciyar kungiya, kuma tana kallonta a zaman kungiyar yan ta’adda.

A hali da ake ciki kuma, ana samun yawan cin zarafi da lalata da mata daga dukkan bangarori dake fafatawa a Syria, ta wajen amfani a mummunar dabi'ar wurin tsoratar da fararen hula da kaskantarwa da kunyatar da mata da suka fada hannunsu,a zaman hanyar hana su magana, a cewar kwamiti kasa da kasa mai zaman kansa wanda yake bincike kan rikicin na Syria.