Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Karbe Ikon Tsakiyar Birnin Afrin Na Syria


Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan

A fafatawar da ake yi tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye da na gwamnati a yankin gabashin Ghouta, kasar Turkiyya ta ce dakarantu sun yi nasarar karbe ikon tsakiyar birnin Afrin.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya ce, dakarun kasar tare da dakarun hadin gwiwa na Syria, sun karbe ikon daukacin tsakiyar Birnin Afrin.

A cewar Erdogan har ma an kafa tutocin Turkiyya a garin.

A ranar Asabar, kungiyar Syrian Observatory for Human Rights, mai kare hakkin dan adam, ta ce sama da mutane dubu 150 sun fice daga muhallansu a yankin Afrin tun daga ranar Laraba.

Rahotannin baya sun ce jiragen sama na Turkiyya sun yi ta lugudan wuta a yankin.

A ranar Juma’a, Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna “matukar damuwarsa, kan yadda ake samun ficewar ‘yan gudun hijira daga yankin gabashin Ghouta da garin na Afrin.

Hakan na faruwa ne yayin da kungiyar nan mai kare yara ta Save The Children, ta ce adadin kananan yaran da suka mutu a bara a yakin na Syria, ya haura na kowa ce shekara, tun da aka fara yakin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG