Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Syria Ya Lashi Takobin Ci Gaba Da Yaki


 Shugaban Syria Bashar al-Assad
Shugaban Syria Bashar al-Assad

Shugaba Bashar Al-Assad na Syria, ya lashi takobin ganin sojojinsa sun ci gaba da kai hari a kan tungar 'yan tawaye ta gabashin Ghouta, duk ko da yake shugabannin Amurka da Birtaniya na zargin sa da kawo wa ayyukan jin kai cikas.

‘’Tilas ne a ci gaba da yaki da ta'addanci, yayin da a waje daya kuma a ci gaba da kwashe fararen hula daga yankin da ake yi, inji Bashar Al-Assad sa'ilin da yake wa manema labarai jawabi wanda aka yayata ta gidan talabijin na kasar.

Yace ba wani rudani tsakanin shirin tsagaita wuta da ayyukan kai farmaki, domin nasarorin da sojojin Syria suka samu jiya da shekaranjiya a Ghouta sun samu ne a karkashin shirin tsagaita wutar.

Assad dai yana amfani da Kalmar ‘yan taadda ne ga ‘yan tawayen dake kokarin ganin sun kifar da gwamnatinsa.

Shugaban Amurka Donald Trump da Prime Ministan Birtaniya Theresa May sun amince a jiya lahadi cewa Rasha da Syria ne hummul haba'isin kawo mummunar koma baya da wahalar da mutane ke sha a gabashin Ghouta. Kamar yadda sanarwar da ta fito daga Ofishin May ke jaddadawa.

Shugabannin sun tattauna ta wayar tarho, a kan abinda ofishin na May ya kira da "halin wayyo ni ALLAH" da ayyukan jinkai suka shiga a yankin. Duk ko da cewa kungiyar nan mai sa ido a wannan yaki, mai babban ofis a Britaniya ta ce sojojin Syria sun karbe ikon fiye da kashi daya cikin hudu, ko rubu'in yankin na gabashin Ghouta.

Amma sanarwar data fito daga fadar shugaban Amurka ta White House ba ta yi bayanin tattaunawar ta wayar tarho ba, amma ta bayyana cewa Rasha tana watsi da yarjejeniyar da kwamitin sulhu na MDD ya bukata na dakatar da bude wuta na tsawon kwanaki 30 a duk fadin kasar Syria.

Sanarwar ta ce Rasha na kashe farar hula da ba su ji ba, ba su gani ba, karkashin inuwar fakewa da yaki da ta'addanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG