Kungiyar Taliban Ta Karyata Cewa Tana Tattaunawar Sirri Da Gwamnatin Afghanistan

Afghanistan

A hukumance, kungiyar Taliban ta fito ta bada sanarwar cewa karya ake mata, ita ba wata tattaunawar asiri da take da gwamnatin Afghanistan, kuma har yanzu tana nan daram kan matsayinta na cewa sai an aiwatarda wasu ka’idoji kafin ta yarda tayi sulhu da gwamnatin.

Daman Jaridar “Guardian” ce ta fito da wannan labarin a jiya Talata, inda ta ruwaito wasu kafofi biyu da bata tantance ko su wane ne ba, tace sun gaya mata cewa an yi tarukka akalla har sau biyu tsakanin sassan biyu a cikin watan Satumba da kuma farkon wannan watan da muke ciki na Oktoba.

Jaridar tace a Doha, babban birnin kasar Larabawan nan ta Qatar aka yi wannan taron, da yake a garin mashawartan Taliban suke zaune.

Shima wani kusar gwamnatin Afghanistan ya tabattarwa gidan rediyon nan na V-O-A cewa lalle an yi taron, koda yake bai bada karin haske kan abinda aka tattauna ba.

Rahottanin suka ce babban shugaban hukumar leken assirai ta Afghanistan Mohammad Masoom Stanekzai ne ya yi jagorancin wannan tattaunawar inda Mullah Abdull Manan Akhnud, kanen tsohon madugun kungiyar ta Taliban, Mullah Umar ya wakilci ita kungiyar ta Taliban.