Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matar Donald Trump Ta Kare Mijinta


Donald Trump da Matarsa Melania
Donald Trump da Matarsa Melania

Mai dakin dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump ta kare mai gidanta daga tofin Allah-wadai da ake yi mashi akan kalaman da yayi na buga kirji cewa yana yadda ya ga dama da mata ko suna so ko basa so, a hira da wani mai gabatar da shiri a talabijin.

A wata hira da aka yi da Melania Trump jiya Litinin a gidan talabijin din CNN, ta fadi cewa mai gabatar da shirin talabijin din Access Hollywood a da Billy Bush, shine ya ingiza maigidanta ya fadi wadannan munanan kalaman wanda aka nada a bidiyo a shekarar 2005. Ta kara da cewa “ba haka maigidanta ya ke ba”. Yana da saukin kai, yana da hakuri, kuma yana mutunta mata.

A bidiyon dai Trump yayi kalaman batsa game da mata; yadda yake rungumarsu da kuma yadda ya so ya nemi wata matar aure. Trump dai ya ba jama’a hakurin wadannan kalaman.

Melania ta fadawa CNN cewa maigidanta ya bata hakuri akan kalaman da yayi, kuma ta gafarta masa. Ta kuma zargi kafafen yada labarai akan yadda suka yada batun don zubda darajar mijinta.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG