Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Cewa Kasar Iraqi Na Kamawa Da Gallazawa Maza Musulmi 'Yan Mazahabar Sunni


Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International tace hukumomin kasar ta Iraq sun dade suna kama mutane, musamman maza Musulmi ‘yan mazahabar Sunni dake gudowa daga yankunan dake hannun ISIS, suna tsare su, suna gana musu azaba, wani lokaci ma har da kashe su, duk a bisa zaton cewa suna da alaka da wadanan kungiyoyin na ‘yan ta’adda.

Kan haka ne kungiyar ta Amnesty take kira akan hukumomin na Iraq da su dauki matakan tabattar da ganin an gujewa wannan dabi’a, wacce kungiyar tace ba dalilin yinta.

Amnesty tace ta samu bayanin wadanan abubuwan na faruwa ne daga hirar da ta yi da mutane sunfi 470 da suka hada da irin wadanan mutanen dake tserowa daga yankunan na ISIS, amma kuma sai a cafke su ana zargin su da cewa suna goyon bayan kungiyoyin na ‘yan tsagera.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG