Kungiyoyin sun tabbatar da cewa sun aike wa kwamitin da mataimakin Shugaban kasa ya nada domin duba yadda za a inganta albashin ma'aikata ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba.
Kwamred Nasir Kabir, shugaban tsare-tsare na kungiyar kwadago ta kasa, ya ce mafi karancin albashin (₦615,000) shi ne abin da suka amince da shi, kuma a kansa za su tsaya, babu gudu babu ja da baya.
Nasir ya ce inda a ra'ayinsa ne, abin da ya kamata a biya ko wanne ma'aikaci ya zama akalla Naira miliyan daya duk wata.
Amma wata ma'aikaciya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce wannan ba abu ne mai yiwuwa ba, domin ko albashin dubu sha takwas da gwamnatin baya ta ce a biya ma'aikata har yanzu wasu jihohi ba su biya ba, balle kuma karin dubu talatin da gwamnatin baya ta yi. In an ce a daga zuwa dubu dari shida har da goma sha biyar, wa zai iya biya? Wannan yaudara ce kawai.
Yusha'u Aliyu kwararre a fannin tattalin arziki, ya ce ba lallai ba ne gwamnati ta amince da wannan bukata, domin za ta auna yawan ma'aikata da ta ke da su da kuma yawan kudin shiga da ta ke samu kafin ta amince. Saboda haka abu ne da zai zama sai an duba da idanun basira, domin a yanzu haka gwamnatin tana da basussuka da dama a kanta.
Ya zuwa yau dai ana bin gwamnatin Najeriya bashin akalla Naira Triliyan 87.9, kuma tuni har ofishin kididdiga ya fito da kiyasin cewa yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 33.20 a watan Maris din 2024 daga kashi 31.70 cikin 100 a watan Fabrairun 2024.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5