Kungiyoyin Matasan Arewa Sun Ba Buhari Wa'adin Kwana 30

Hadakar kungiyoyi matasa masu zaman kansu a Najeriya sun gudanar da wani taro, akan tabarbarewar tsaro a Arewacin kasar.

Taron wasu kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya, sun bayyana cewar sun gaji da jan kafar da gwamnati ke yi gameda magance matsalar tsaro a yankin.

Kungiyoyin sun kira taron gaggawa a jihar Kaduna saboda maganar tabarbarewar tsaro karkashin jagoranchin (Joint Action Committee of Northern Youth Associations) a turance, sun baiwa shugaban Kasa makonni biyu ya kawo karshen matsalar tsaro a yankin, ko kuma a baiwa al'umma damar kare kawunan su. Kwamrade Murtala Abubakar shine Jagoran wadannan kungiyoyi.

Yana mai cewa "Ya kamata shugaban kasa ya maye gurbin manyan habsoshin tsaron kasar, kana shugaban ya gaza kare al'ummahr kasar kamar yadda ya dau alkawali, haka sun bashi wa'adin kwanaki 30, kodai ya kawo karshen matsalar nan ko kuma yayi murabus. Babban abu shine a yiwa bangaren tsaro garon bawul."

Ya kara da cewa "Idan gwamnati ta gaza to ya kamata ta baiwa 'yan kasa damar karen kansu, sai kuma akwai bukatar Sifito janar ya sake duba dokar hana mallakar makami ga 'yan kasa, a baiwa 'yan kasa da aka aminta da su damar mallakar bindiga. Saboda 'yan ta'addar nan suna dauke da manyan makamai, kaga kuwa mutane zasu so su samu tsaro mai inganci."

Sai dai kuma masana harkokin tsaro na ganin mallakar makamai ba zai haifawa Najeriya da-mai-ido ba. Kamar dai yadda Dr. Yahuza Ahmed Getso ya nunar.

Yan ganin kuwa "Idan aka ce jama'a su dinga mallakar bindiga, to za'a dinga samun matsaloli na rashin tsaro a cikin jama'a, a duk lokacin da aka samu rashin jituwa a cikin al'umma, to za'a iya amfani da wadannan makaman wajen tada zaune tsaye."

Ita kuwa gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya CNG na ganin maganar matsalar tsaron taron dangi ta ke nema. Kwamrade Abdul'Aziz Suleman shine mai magana da yawun kungiyar na Kasa.

Ya ce "Azo a zauna a fitar da hanyar da za'a hada kan kasa, babu dalilin da zai sa idan an dai-daita da mutanen na a jihar Zamfara sai ka gansu sun koma jihar Katsina. Sai an fitar da hanya daya da duka jihohin nan zasu dinga aiki baidaya, wanda ta haka za'a iya shawo kan matsalar."

Kwamrade SonAllah Ishiyaku na Kungiyar matasan Arewa daga Bauchi ya na da mabanbanchin ra'ayi. Inda ya ke cewa " Mun zabi Buhari da tunanin cewar zai kare mu baki daya, amma a yanzu ya gaza, ai lokacin da aka zabe shi kowa yana tsoron shi, amma daga bayan mun gane cewar a she Zakin ma ba shi da hakori."

Sai a saurari rahoton Isah lawal ikara a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Matasan Arewa Sun Baiwa Buhari Wa'adin Kwana 30