Tun a daren ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a kauyukan Gada da Karakka, a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
‘Yan bindigan dai sun dauki tsawon lokaci suna harbe-harbe don razanar da jama’ar yankin.
Wani mutum da ya tabbatarwa Muryar Amurka aukuwar lamarin ya kuma bukaci a sakaya sunansa, ya ce, "tun a jiya da tsakar dare misallin karfe 1:00 saura na dare aka buga musu waya da cewar, ‘yan bindigar sun isa kauyen Gidan Daji, sun kuma tarkata shanaye da sauran dabbobi, har zuwa sauran kauyuka da suke makwabtaka da su."
Rahotanni sun ce maharani sun dauki lokaci mai tsawo suna harbe-harbe, lamarin da ya sa mutane suka bar kauyukan don neman kubutar da rayuwarsu, daga baya, ‘yan bindigan sun isa kauyen Gada, nan ma suka kwashe shanu, daga nan suka wuce garin da ake kira Dabar Maradun, nan ma suka kwashi dabbobin jama’a.
A cewar Malamin, wannan lamarin ya zama ruwan dare wanda duk bayan kwana biyu ana samun aukuwar wannan aikin ta’addancin, har ma a yanzu ana iya cewa abun ya zama jiki.
Tun da tsakar dare ake ta bude wuta a tsakanin ‘yan bindigan da wasu mayakan garin masu kare kai, har zuwa wayewar garin ranar Alhamis.
Sun sanar da mahukunta halin da ake ciki, kuma an tura jami’an tsaro don kai karshen matsalar.
Don samun karin bayani sai a saurari tattaunawar Sani Manumfashi da mai ba da rowan mazaunin yankin: