ABUJA, NIGERIA -A hirarta da Muryar Amurka, shugabar kungiyar Madam Florence Edward ta bayyana cewa, sun fi son Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu goggagen masanin harkokin noma kuma wanda yake da alaka da manoma domin jagorantar harkar noman kasar yadda ya kamata.
Florence ta ce an kwashi shekaru da dama ana cewa gwamnati tana tallafawa harkar noma amma har yanzu manoma ba su gani a kasa ba.r
Shi kuwa Shugaban Manoman Masara ta Kasa Bello Abubakar Anur ya nuna cewa hanya daya da za a iya farfado da tattalin arzikin kasar ita ce ta inganta harkar noma.
Annur ya ce kungiyar tana son gwamnati ta fahimci cewa, akwai matsaloli da dama da manoma ke fuskanta musamman ma a yanzu da aka janye tallafin man fetur.
A nashi jawabin Shugaban Kungiyar masu fatauci, kiwo da sarrafa naman saniya ta kasa Iliyasu Bulama ya yi tsokaci cewa da dadewa ana magana ne akan Makiyaya da Fulani, amma kuma duk ba a fahimci inda matsalar ta ke ba.
Iliyasu ya ce matsalar tana wajen mai kiwon saniya ne, saboda ba a killace masu wurin da ya kamata su zauna ba. Iliyasu ya kuma cewa yadda noma ya zama wajibi haka kiwo ya zama wajibi, saboda haka yana kira ga Gwamnati da ta yi kokarin magance rashin jituwa da ke wanzuwa tsakanin Makiyaya da Manoma ta hanyar killace su makiyayan saboda a yi maganin yawan matsalolin tsaro da ke tasowa a tsakaninsu.
Kwararre a fannin zamantakewan dan Adam kuma mai nazari a al'amuran yau da kullum Abubakar Aliyu Umar, yana ganin ba a nan gizo ke saka ba, saboda yawancin wadanda ake nada wa Ministocin Kula da harkar noma, gogaggu ne a fanin noman.
Abubakar ya ce son kai, da kwadayi, da almundahana ne ya yi katutu a zukatan mutane shi ya sa ba sa ba harkar noman kyakyawar kulawa. Abubakar ya ce, mutum mai rikon amana, kuma wanda ya san ya kamata, marar kwadayi, shi ne kawai za a nema a cikin kasa, sai a nada shi Ministan kula da harkar noma, idan an yi haka, to kasa za ta wadatu da abinci har ta sayar a waje.
Kungiyoyin sun ce za su yi hadin gwiwa a matsayin gudumawarsu tare da fitar da sabbin dabarun noma da fasahohin zamani domin kawo sauyi a fannin kayayyakin amfanin gona a Najeriya
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5