Kungiyoyin Kare Muhalli Da Hukumomin Nijer Sun Yi Zaman Tsare Tsaren Halatar Taron COP 26

A jamhuriyar Nijar, kungiyoyin fafitikar kare muhalli sun gudanar da wani taron hadin gwiwa da jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin kasa da kasa.

An gudanar da taron ne domin bitar halin da ake ciki game da alkawuran da kasar ta dauka a taron kare muhalli na duniya da aka yi a birnin Paris a 2015 a matsayin wani bangare na shirin halartar taron COP 26 da kasar Birtaniya ke karbar bakuncinsa a watan November 2021.

Al’ada ce a wajen kungiyoyin kare muhalli na cikin gida Nijer da na kasa da kasa kan kira taron tantaunawa da hukumomin kasar don bitar ayyukan da suka gudanar a bisa la’akari da alkawaluran da gwamnatocin ke dauka a yayin taron kasashen duniya kan batun canjin yanayi mafarin gudanar da wannan taro da ke matsayin na shirye shiryen taron COP 26 da za a yi daga ranar 1 zuwa 12 ga watan November 2021 a birnin Glasgow na kasar Britania, a cewar shugaban hadin gwiwar kungiyoyin kare muhalli na PFSCO CC DD Lawali Malan Karami yayinda yak e bayani wa manema labarai.

Wani rahoton binciken wata cibiyar kasa da kasa ya ayyana cewa dumamar yanayin da ake fama da ita za ta haifar da hauhawar ma’aunin yanayin zafi da degre celcius 1.5 daga shekarar 2030 lamarin da ka iya janyo illoli da dama akan muhalli yayinda a daya bangare bayani ke nunin kasashe da dama na jan kafa a game da alkawuran da suka dauka a taron Paris na 2015.

Wakilin ministan kare muhalli a wannan zama na share fagen zuwa taron Glasgow Mahaman Sani Massallatchi ya bayyana cewa, wannan haduwa na da mahimmanci sosai a wajen gwamnatin Nijer domin za ta kasance wata damar tayar da masu hannu da shuni daga barci game da gudunmuwar da ake fatan samu daga gare su don tunkarar kalubalen da duniya ke fama da shi sakamakon dumamar yanayi.

Jamhuriyar Nijer dake tsakiyar yankin Sahel na daga cikin kasashen da suka fi dandana kudar matsalolin canjin yanayi a duniya lamarin da a fili ake gane koma bayan da ya haddasawa ayyukan noma da kiwo kuma yake barazana ga rayuwar jama’a a dalilin gurbacewar iskar da ake shaka yayinda ake ci gaba da fuskantar kwararowar hamada da zaizayar kasa da matsanaciyar ambaliyar ruwa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Kare Muhalli Da Hukumomin Nijer Sun Yi Zaman Tsare Tsaren Halatar Taron COP 26