A Najeriya masana na ganin rugujewar tasiri da martabar kungiyoyin fafatuka na daga cikin abubuwan da suka baiwa ‘yan siyasa damar mike kafafuwa su shimfida mulki ta yadda suka ga dama ba tare da an kalubalance su ba.
Wannan na zuwa ne lokacin da wasu kungiyoyin suka farga suka soma tunanin lalabo hanyoyin farfadowa da kimar su ta yadda watakila za su iya samar da alkibla ga samun kyakkyawan tsari ga dimokradiyar kasar.
Bayanai dai sun nuna cewa a kasashen duniya daban-daban har ma wadanda suka ci gaba kamar Amurka, Ingila da Faransa, kungiyoyin fafatuka sun bayar da gagarumar gudunmuwa ga ‘yanto jama'a daga matsaloli tare da yin alkibla ga wanzuwar kyakkyawan shugabanci.
A Najeriya ma, irin wadannan kungiyoyi su ne suka yi ta fafatuka har suka nemowa kasar ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
“Kyakkyawan tsarin dimokradiya yakan samu idan an samu irin wadannan kungiyoyi da kan iya jajircewa su yi wa gwamnati matsin lamba sai ta yi abin da ya dace wanda ‘yan kasa ke muradi.” In ji masanin kimiyar siyasa aFrfesa Tanko Muhammad Baba.
Shi ma Farfesa Bello Daudun Badah, yana ganin cewa “ irin wadannan kungiyoyi suna da gudunmuwa da za su iya bayarwa kasancewar su ne mafi hulda da mutane har a matakin karkara don suke iya sanin bukatu da kuma wayar da kan jama'ar”.
Yanzu da yake kungiyoyi masu gwagwarmaya sun farga kuma suna son samar da sauyi akan wannan lamarin, masu lura da al’amurran yau da kullum kamar Barrister Mu'azu Liman Yabo masanin dokokin kasa, na ganin abu ne mai kyau muddin za'a dage.
Masana dai na ganin muddin kungiyoyin fafatuka za su kalubalanci jam'iyun siyasa akan su fito da akidodi wadanda za su kai kasar ga ci gaba kuma suka yi tsayin daka jam'iyun su yi aiki da akidodin, to lallai matsalolin da suka dabaibaiye Najeriya suna dab da zama tarihi.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sokoton Najeriya:
Your browser doesn’t support HTML5