Kungiyoyin dai sun kudiri aniyar daukar mataki idan har gwamnati ta gaza wajen zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan laifin tare da hukunta su.
Biyo bayan halin rudani da al’umma arewacin Najeriya suka shiga sakamokon mummunan kisan gillar da aka yi wa matafiya sama da ashirin da ake zargin wasu matasa ne suka aikata a yankin Jos ta arewa da ke jihar ta Filato, kungiyoyi da dama daga arewacin kasar sun bukaci a gaggauta zakulo wadanda ke da hannu kan wannan aika-aika ko kuma su dauki mataki.
Alhaji Abdulrahaman Buba Kwacham shi ne shugaban kungiyar matasa ta Arewa maso gabas da aka fi sani da Movement of North East Youth Organisation Forum a turance,
A cewarsa wannan al'amari, abu ne wanda ba za su yarda da shi ba kuma ba za su bari abin ya wuce haka ba.
Ya kara da cewa duk mai hankali ya san an yi ba daidai ba, kuma idan da za a sa bidiyo don wadanda suka aikata hakan su gani, da za su ji tsoron abin da su ka yi.
Ita ma gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya ta bakin shugaban ta Nastura Ashir Sherif, ta bayyana cewa duk mutumin da ya zo arewacin Najeriya ya na cikin fargaba.
"Duk mutumin da yake arewa maso gabashin Najeriya yana cikin fargaba Idan ya zo Abuja zai koma gıda, saboda wannan jihar Filato yadda suka mayar da wannan abin, kamar ba laifi ba ne su tare hanya su kashe mutane su kona dukiyarsu saboda ba a taba hukunci akan wannan al'amari ba." In ji Nastura.
Kungiyar Ahanas mai rajin zaman lafiya da ci gaban al’umma a jihar ta Filato da kewaye ta bakin shugabanta Alhaji Abdullahi Musa, ta ce idan ba’a gaggauta daukar mataki ba to ba shakka za’a dawo da hannun agogo baya a karamar hukumar da ake farin cikin zaman lafiya ya samu.
Jihar Filato dai na da tarihin rikici mai kasaba da kabilanci da na addini, kuma a ranar Laraba ne al’ummar Musulumai a Jos ke shirin yin tattaki zuwa majalisar dokokin jihar a wani mataki na kira ga gwamnati da ta kawo dauki ga al’ummar jihar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5