Ana saura kwana daya ‘yan Najeriya su nufi rumfunan zabe,domin zaben shugaban kasa,wani kamfanin fina finai da ake kira “Juju” ya saka wani fefen vidiyo a dandalin U-Tube, wadda ya nuna jami’an hukumaer zabe suna tafka magudi jihar Rivers.
Ana danganta nasarar haka ga kafofin sadarwa na zamani dake kara karfafa guiwar kungiyoyin tallafi masu zaman kansu wajen tabbatar da ingancin zabe a Najeriya.
Wan nan vidiyo da aka nuna a dandalin U-Tube ranar Alhamis ya nuna jami’an aikin zabe a jihar Rivers ta Najeriya suna tafka magudi a zaben wakilan majalisa da aka kammala makon jiya.
Karkashin vidiyon har da lambar woyar cellular wani wakilin hukumar zabe domin baiwa ‘yan Najeriya da dama ko ina suke a Duniya, zarafin kiran hukumar domin yin korafi kan abinda suka gani.
A wani lamari a birnin Washington bada jumawan nan ba,Reno Omokri, ya yi bayani kan matakanda kungiyarsa mai inkiyar CYE ko Council for Youth Empowerment a najeriya take karfafa guiwa ‘yan kungiyar su dauka.
Yana cewa “kaje ka cikin tsanaki kana daukar vidiyon abinda yake faruwa, san nan ka nunawa duniya,dominn a tilasta gudanar zabe sahihi mai inganci. Ba zamu dogara da hukumar zabe ta INEC ba.
Omokri yace, suna tura matasa ‘yan Najeriya daga nan Amurka,Ingila da wasu sassan duniya domin su sa ido kan zaben.