Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejjeniyar tsaida dan takara guda tsakanin jam’iyyun CPC da ACN a zaben shugaban Nigeria ta wargaje


Muhammadu Buhari (File photo)
Muhammadu Buhari (File photo)

Yarjejjeniyar hada kai domin tsaida dan takarar shugaban kasa guda a tsakanin jam’iyyun siyasar Nigeria, CPC da CAN ta wargaje ba tare da an cimma daidaituwa ba. Makasudin yarjejjeniyar shine a sami hadin kan gungun jam’iyyun hamayyar Nigeria da zasu iya tinkarar jam’iyyar PDP mai mulkin Nigeria a zaben ranar Asabar mai zuwa.

A jawabin da shugaban jam’iyyar ACN ya yiwa taron manema labarai a shalkwatar jam’iyyar CAN ta kasa a birnin Abuja, shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon Gwamnan jihar Osun dake Kudu Maso yammacin Nigeria, Chief Bisi Akande, bai bada wani kwakkwaran dalilin da tattaunawar hadin kan jam’iyyu biyu ya wargaje ba tare da an kai ga cimma daidaituwar tsaida dan takarar shugaban kasa guda ba.Amma ya furta cewar bayan an kammala zaben shugaban kasa a ranar Asabar ba’a sami fidda dan takarar day a sami Nasara a lokaci guda ba, lokacin ne jam’iyyar CAN zata san irin matakin da zata dauka. Amma shugaban na jam’iyyar CAN ya kumayi zargin rashin samun cikakken hadin kai daga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar CPC kuma tsohon shugaban Nigeria Janar Muhammadu Buhari.

A halin da ake ciki, ‘yan Nigeria sun fara bayyana ra’ayinsu game da rashin samun nasarar yarjejjeniyar tsaida dan takarar guda daga jam’iyyun CAN da CPC, a rahoton da wakilin mu a birnin Ibadan yammacin Nigeria Hasan Umaru Tambuwal ya aiko mana, mafi yawan al’ummar Yammacin Nigeria, Yarabawa da hausa sun nuna takaicin hakan.

XS
SM
MD
LG