Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasikun Ra’yin Masu sauraren Sashen Hausa na Muryar Amurka VOA Jumma'a, 15 Afrilu 2011


Wasu 'yan Nigeriake nan zaune a karkashin gada dauke da takardun gangamin zabe na Fasta a Ojuelegba jihar Ikkon Nigeria.
Wasu 'yan Nigeriake nan zaune a karkashin gada dauke da takardun gangamin zabe na Fasta a Ojuelegba jihar Ikkon Nigeria.

Zaben 2011 na Najeriya

Mai sauraren mu Malam Nura Dalhatu Audu Sabon Garin Gashua jihar Yoben Nigeria a yau Juma’a 15 ga watan Afrilun shekarar 2011 Miladiyya 15/04/2011 shine ya rubuto wasikar dake cewa zaben jam’iyyar CPC a karkashin Janar Muhammadu Buhari, shine zaikawowa Nigeria ci gaba da kubutar daTalaka daga kangin Azzaluman Nigeria. Shi kuma Malam Umaru S. Gardi Maradun, ya aiko datashi wasikar ce dake cewa VOA ku gayawa Janar Buhari ya daina wahalar da kansa da batun kare talakawan Nigeria domin zaben day a gabata ya nuna bamu gaji da wahalar da kangin bauta ba, don haka ka barmu da wadannan Azzalumai, haka muke so haka muka zaba. Ka huta ma kanka, kada hawan jinni ya kamaka a banza. Shi kuwa MalamAbubakar dan Auta a hirar da aka yi dashi yana cewa, to mutanen jihar Kebbi, kunga yadda zaben satin day a wuce ya kasance, ina fatan zaben gobe kada a barku a baya. Shi kuwa Malam Bala na yashi Anguwar yashi Lakwaja ya aiko da wasikar dake cewa a yanzu ta leko ta koma kawance tsakanin jam’iyyun siyasa ya kau, fatan mu shine ‘yan Nigeria, zaben gobe na shugaban kasa, mu fito sosai domin zaben shugaban da zai kaimu Tudun Mun tsira saboda son kai yasa jam’iyyun Adawa sun kaimu sun baro wannan abin takaici ne. 15/04/2011

Ita kuwa Fadima Ahmad Matar Aminu Abdu Bakanoma Sani Mai-Nagge Kano Nigeria ta aiko da wasikar dake cewa ina kira ga ‘yanuwana ‘yanNigeria musamman mata ya kamata idan kunje jefa kuri’a, akula da kyau wajen Dangwalawa, kada ku bari ta lalace, kar kuma kumanta kuri’arku itace ‘yancinku. 15/04/2011

Shi kuma Malam Khamisu Shehu Jazuli Gamawa, jihar Bauchin Nigeria ya aiko da wasikar dake cewa yau inaso ne nayi kira kuma tare da yin fadakarwa ga mutumin da ake yiwa krari da “Kakakin ‘yan Adawar Nigeria” wato Injiniya Buba Galadima dangane da irin maganganun da yake yi tare da kawo rudani a jam’iyyar CPC, domin kuwa mu talakawa mun fahimci cewa irin rikice-rikicen ‘yantakarar Gwamna da suka faru a jihohin Kano da Katsina da kuma Bauchi a halin yanzu rahotanni sun nuna cewar akwai hannun Buba Galadima dumu-dumu. 15/04/2011

Shi kuma Malam HamzaGaladima Birnin Kebbi ya aiko da wasikar dake cewa inakira ga hukumar zaben Nigeria da cewa ya kamata ta dauki kwakkwaran matakin bincike dangane da zaben ‘yan majalisun da aka gudanar makon jiya a jihar kebbi. 15/04/2011

Shi kuwa Malam Zaidu Bala Kofa sabuwa Birnin kebbin Nigeria ya aiko da wasikar dake cewa ina son inyi kira ga ‘yanuwana al’ummar jihar kebbi da Sokoto da Zamfara da kano da naija a kan abinda suka yi lokacin da aka yi zaben share fage tsakanin Atiku Abubakar da Goodluck Jonathan- kowa ya san ‘yan wadannan jihohi sun yi abinda ya burge al’ummar Arewa sannan yanzu babu jihohin da aka fi zubawa ido kamar su a zaben gobe, domin ba zamu bari wasu mayaudaran ‘yan siyasa sake yaudararmu ba. 15/04/2011

Sai kuma wasikar da ta fito daga wajen Malam Ka’abu Abubakar Zage dake cewa Allah ya kawo mu lokacin da mu talakawa zamu yiwakanmu kiyamul laili mu fito mu fito zaben gobe don mu sauya wannan gwamnati ta PDP wacce ta shafe shekaru 12 tana azabtar damu. 15/04/2011

XS
SM
MD
LG