Mr. Jonathan yana fuskantar kalubale daga manyan ‘yan takara biyu na jam’iyyun hamayyar da suka kasa cimma daidaituwar hadin kai a zagayen karshen tattaunawar da suka yi. Manyan masu kalubalantar Jonathan biyu sun hada da tsohon shugaban Gwamnatin mulkin sojin Nigeria, janar Muhammadu Buhari, da kuma tsohon shugaban hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta Nigeria, Nuhu Ribadu.
Mr. Jonathan dake rike da ragamar mulki a yanzu yayi alkawari a yakin neman zabensa cewar zai dauki matakan inganta tattalin arzikin Nigeria, zai kuma inganta ayyukan kiwon lafiya da bunkasa ilmi. Shi kuwa abokin takararsa Muhammadu Buhari ya dauki alkawarin idan har ya sami nasara aka zabeshi zai dauki matakan tabbatar da kauda cin hanci da rahsawa a Nigeria, yace za’a kuma kora sake farfado da masana’atu da inganta hanyoyi da bunkasa hanyar sadarwa da sufuri. Shi kuma Nuhu Ribadu yayi alkawarin bada fifiko wajen yaki da talauchi domin kauda ‘yan Nigeria daga masifar fatara da yunwa. Hukumomin tsaron Nigeria sun karfafa daukan matakan tsaro tun daga Juma’a domin hana afkuwar tashin hankali a lokacin zaben, an kuma rufe kan iyakokin Nigeria dukan baza soja suna gadi.