A sanarwar da suka fitar ta bakin Malan Mahmoud Ousman mai Magana da yawun wadanan kungiyoyin addinin Islama, sun ce yunkurin da gwamnatin ta Nijer ta sa gaba ta hanyar wadanan kudirori da ta aikewa majalisar dokokin kasa da sunan karfafa matakan samar da ci gaban al’umma wani abu ne da bai dace da tsarin zamantakewar jama’ar Nijer ba a ko al’adance ko a addinance saboda haka suka bukaci mahukunta su canza tunani.
Wani sashe na kudirorin da ke gaban majalissar na kunshe da matakin hana kiran salla a Nijer inji wadanan malamai.
Kawo yanzu gwamnatin kasar ba ta yi bayani ba dangane da wadanan koke koke to amma kuma bayanai sun yi nuni da cewa a jiya alhamis ne ya kamata majalisar dokokin kasa ta nazarci wannan batu kafin a sanar da cewa an dage zaman zuwa wata ranar da ba a bayyana ba tukuna. Da take amsa tambayoyin da Muryar Amurka ta yi mata kan wannan lamari ‘yar majalisar dokoki Honorable Nana Jubi Harouna Mati ta bukaci ‘yan Nijer su kwantar da hankalinsu domin majalissa zaure ne na wakilicin al’umma.
A jawabinsa na ranar matan Nijer ta 13 ga watan mayun da ya gabata shugaban kasa Mohamed Bazoum ya ja hankulan ‘yan kasar akan maganar saka tsari a zamantakewar iyali don kaucewa haifuwar ‘yayan da ba za iya daukan dawainiyarsu ba sakamakon talaucin da ake fama da shi a Nijer haka kuma yayi gargadi akan rashin dacewar tara mata barkatai ga masu karamin karfi abinda ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya daga wajen al’umma saboda a cewarsu wadanan shawarwari sun sabawa addinin musulunci.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5