Cikin irin badakalar data faru a baya bayan nan ta hada da zargin aikata ba daidai ba da Sanata Isa Hamma Misau, ya yi wa Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Duka batutuwa ne da ke nuna irin halin da kasar ke ciki.
Abin da yafi daga hankalin kungiyoyin shine barazanar da suka ce wannan na yiwa majalisar zartaswa, matsalolin cikin gida dake ci gaba da kunno kai cikin gwamnatin demokaradiyyar kasar, Ko mai ya ja hankalin kungiyoyin a yanzu musamman a batun da ya shafi sufeton ‘yan sandan Najeria?.
Malam Ibrahim Modibbo, shine shugaban kungiyar ‘yan Najeriya masu nuna damuwa da demokaradiyyar kasar ya bayyana cewa zargin sufeton ‘yan sanda da cewa yana karbar Biliyan goma a kowane wata ba tare da kowa ya sani ba a lokacin wannan mulkin na Buhari, bai yi dai dai ba.
Haka kuma daya daga cikin sanatocin dake binciken zargin da Isa Hamma Misau, ya yi, sanata Abdul’aziz Nyako, ya ce majalisar dattawa tana da hurumin bincike musamman idan batun ya shafi cin hanci da rashawa.
A daya bangaren kuma, batun zargin badakalar data faru a bangaren man fetur bayan nunawa juna yatsa, da rubuce-rubuce tsakanin babban daraktan kamfanin man fetur na NNPC da ministan kasa a ma’aikatar mai ta Najeriya, lamarin ya fra jan hankalin al’ummar kasar, musamman ga batun yaki da cin hanci da rashawa.
Domin cikakken bayani saurari rahoton Medina Dauda a nan.
Your browser doesn’t support HTML5