Jihar Benue ta fi kowace jiha a Najeriya, fuskantar ambaliyar ruwa lamarin da ya raba dubban jama’a da muhallansu, baya ga asarar dukiya da rayuka.
Ta dalilin haka ne ma’aikatar ruwa ta gwamnatin tarayya ta tura kwararru a jihar ta Benue domin gano musabbabin faruwar hakan.
Injiniya Suleman Hussaini Adamu, shine ministan albarkatun ruwa na Najeriya, ya bayyana cewa binciken ya nuna cewa shekaru da dama da suka gabata, kogin Benue, ya canza hanya a sanadiyyar haka ne jama’a suka yi gine gine a kan tsohuwar hanyar da ruwan yake wucewa a da.
Kwararre kan muhalli Ibrahim Musa, ya dora alhakin samun yawan ambaliyar ruwa akan jama’a da kuma gwamnatoci, ya kuma bayyana cewa zubar da ledoji da shara a magudanan ruwa da hukuma ta gina da kuma gine gine kan magudanan ruwa duk na daga cikin dalilan dake haifar da ambaliyar ruwa.
Domin karin bayani ga rahoton Hassan maina kaina daga Abuja.
Facebook Forum