Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta kasar Amurka zata taimakawa jihar Neja kan bunkasa kiwon lafiya a jihar a matakin farko.
Gidauniyar zata horas da jami’an kiwon lafiya da zasu dinga aiki a assibitocin yankunan karkara.
Shugaban Gidauniyar, Dr Chris Elias, ya jadadda muhimmancin maida hankali akan kiyon lafiyar al’umma a koda yaushe, kuma wannan shine aka fi baiwa mahimmanci a yarjejeniyar tasu da gwamnatin jihar Neja.
A karin hasken da ya bada, Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, yace da farko zasu horas da ma’aikatan kananan asibitoci. Yace a shekarar farko gwamnatin jihar zata biya kashi ishirin na kudin horas da ma’aikatan, gidauniyar kuma ta biya sauran kashi tamanin, yayinda a shekara ta biyu jihar zata biya kashi talatin. Gwamnan yace haka zasu dinga yi har komi ya dawo hannun gwamnatin.
Daga karshe tawagar gidauniyar da ta gwamnan jihar da ta ministan kiwon lafiyar Najeriya, Farfesa Isaac Adewale, sun isa kauyen Fuka inda aka samu bullar cutar zazzabin masassharar Lassa a kwanakin baya domin bude wani asibitin da gwamnatin tarayya ta gina.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum