Baya ga matsalar karanci da kuma rashin biyan albashi ga malamai, yanzu kuma wata matsalar dake addabar harkar ilimi musamman a jihohin arewa maso gabas itace ta rashin Malamai a makarantun karkara.
Wannan matsalar ta rashin malamai a yankunan karkara yanzu haka tana neman durkusar da harkar ilimi a wasu yankuna musamman a jihohin arewa maso gabas da tashin hankalin Boko Haram tafi shafa.
Don zaburar da wadanda ke karantarwa, yanzu haka Hadakar Kungiyar Malamai ta Najeriya, NUT, ta soma karrama wasu malamai dake bada tasu gudummawa, kamar yadda aka yi a jihar Adamawa inda a kwanan nan NUTta karrama wani shugaban makarantar firamare bisa namijin kokarin da yayi na daukan nauyin biyan wasu malaman wucin gadi albashi daga cikin dan albashin da yake samu.
Comrade Rodney Nathan dake zama shugaban kungiyar malaman a jihar yace sun dauki matakin ne domin karfafa gwiwar sauran malamai masu nuna irin wannan kwazon.
Shi dai wanda aka karraman, Mr Bulaube Myadumiya, dake karantarwa a makarantar firamare ta Bwashi, yace ya dauki wannan mataki ne ganin matsalar da suke fuskanta a makarantu dake karkara.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum