Kungiyar Tallafawa Marayu Da Gauraye Tayi Tsokaci Kan Dokar Ta Baci

Kofa dake shiga birnin Maiduguri a Jihar Borno, Mayu 19, 2013.

Kungiyar Tallafawa Marayu Da Gauraye ta Musulunci ta soki yadda gwamnati ta aiwatar da dokar ta baci saboda yadda dokar ta shafi mata da yara.
Hajiya Rabi’atu Sifiyan Ahmed, shugaban kungiyar tallafa wa marayu da gauraye ta Musulunci, tace mata da ‘ya’yansu sun fi wahala, saboda gwamnati bata yi la’akari da talaucinsu ba a jihohin da aka kafa dokar ta baci.

A cewar Hajiya Rabi'atu, rashin samar da kayan abinci ga mata, musamman ma marasa maza zai saka su a cikin halin wahala, su da 'ya'yansu.

Ta ce "Gwamnati da kalli dokar, ta tausaya wa mata saboda sun bada gudunmuwa mai tarin yawa dangane da shugabanci, da zaman lafiya, da tarbiyya, da cigaban Najeriya baki daya."

Hajiya Rabi’atu ta kara da cewa hanyoyin da ake bi a yanzu wajen warware tarzoma da tashe-tashen hankula, ba sune zasu cimma nasar ba. Mrs Ahmed ta cigaba da cewa dokar hana fita waje ta takurawa mata wadanda ke da yara, kuma basu da maza ko hanyar samun abinci.

Ran Talatan makon da ya wuce ne, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, domin korar 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar nan ne da ake kira Boko Haram.

Your browser doesn’t support HTML5

Hirar Ibrahim Ka'almasih Da Hajiya Rabi'atu Ahmed