Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Najeriya Dari Biyu Sun Isa Adamawa


Sojojin Najeriya a kasar Mali.
Sojojin Najeriya a kasar Mali.

Yau fa kwana shida kennan da kaddamar da dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, kuma sojojin Najeriya na cigaba da kutsawa cikin wadannan jihohi.

WASHINGTON, D.C - A jihar Adamawa, wakilimu Ibrahim Abdulaziz gane wa idannunsa wadannan sojoji, kimanin sojoji 200 wadanda za’a aika wurare dabam-dabam

Babban kwamandan rundunar soji na 23 dake Yola, Brigadier Janar Fatah Oladipo Ali ya karbi sojojin inda yayi musu kashedi, da suna sanin yakamata, saboda kaucewa wuce-gona-da-iri.

Kwamandan ya gargadi sojojin musamman, akan kar su zubar mutuncin sojan Najeriya.

Da misalin karfe uku na rana, wakilin Muryar Amurka a can Adamawa Ibrahim Abdulaziz ya ga mutane na kokarin komawa gida, saboda gudun kar lokacin shigowar dokar-hana-fita ya kama su a waje.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG