A garin Maiduguri ran Asabar, sojoji sun kafa dokar takaita zirga-zirga na sa’o’i ashirin da hudu a wasu unguwanni goma sha biyu. Sai jiya sojojin suka dan yi sassauci.
Bisa ga sanarwar da sojoji suka fitar mutane na iya fita daga karfe bakwai na safe zuwa karfe biyar na yamma. Wannan lamarin ya shafi harkokin kasuwanci da na yau da kullum.
Masu sayar da katin salula sun koka da dokar. Wani da aka zanta da shi yace kafin dokar ya kan sayar da kati na kusan nera dubu talatin ko fiye ma. Sai yau an wayi gari ko sisin kwabo baya samu. Bugu da kari ita kafar salula din hukumomi sun rufeta bayan an yi shekaru goma ana anfani da wayar salula.
Makarantu ma basu tsira ba. Wani da aka zanta da shi yace tun da aka kafa dokar makarantu suke rufe sai ranar Laraba da ya kai dansa da safe amma karfe goma sha daya na yi aka kirawo shi ya dauki dansa. Masu aikin sufuri su ma sun samu cikkas. Babu wurin anfani da hanayar sadarwar yanar gizo sai mutane sun bi dogon layi a gidan gwamnati.
Ga rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Biu ya aiko domin karin bayani.