Kungiyar SERAP Ta Bukaci Kamfanin NNPCL Ya Fito Da Bayanan Adadin Gangar Danyen Man Da Yake Haka A Duk Rana

SERAP

Kungiyar kare yancin 'yan kasa da kuma kididdigar ayyuka ta SERAP, ta umarci babban kamfanin albarkatun man-fetur na NNPCL da ya  bayyanawa 'yan kasar adadin gangar danyen man da suke haka a duk rana.

Sun kuma bukaci su fito da bayanan ribar da kasar ta samu bayan cire tallafin man-fetur da kuma yadda NNPCL ta ce ta kashe naira tiriliyan 11 a matsayin tallafin man-fetur.

Kungiyar kare yancin 'yan kasa da kuma kididdigar ayyuka ta SERAP, ta umarci babban kamfanin albarkatun man-fetur na Najeriya NNPCL da ya fito ya bayyana wa yan kasa adadin gangar danyen albarkatun mayi da suke haka a duk rana kuma suke fitar wa kasuwar duniya.

A sanarwar da ta fitar ta hannun mataimakin daraktan kungiyar Kolawole Oluwadare, kungiyar ta umarci shugaban kamfanin na NNPCL Mele Kyari, ya bayyana wa yan kasar yawan kudaden da kamfanin ya samu biyo bayan cire tallafin man-fetur a watan Mayun 2023.

Mele Kyari

SERAP, ta kuma bukaci Mele Kyari ya fito ya bayyana yadda suka biya Naira triliyan 11 a matsayin tallafin man-fetur, ya kuma wanke zargin da ake yiwa kamfanin NNPCL na rashin saka kudin danyen albarkatun mai da suka sayar zuwa babban asusun kasar.

Kungiyar, ta ce "bayyana wa yan kasa yadda aka sarrafa kudaden na danyen albarkatun mai, shine hanya mafi dacewa domin kaucewa zargi. Rashin yin hakan ka iya saka zargi da rashin yarda a zukatan yan kasa.”

Kazalika, kungiyar ta ba kamfanin na NNPCL kwanaki 7, domin kididdigar dukkanin zargin da ake musu, idan kuma ba haka ba, kungiyar zata dauki matakin shari'a, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

Idan za'a iya tunawa a makon da ya gabata, tsohon gwamnan babban Bankin Najeriya CBN Sanusi Lamido Sanusi, yayi ikirarin cewa, kamfanin NNPCL bai sa kudade gangar man da ya sayar zuwa babban asusun kasar ba, ya kuma nemi sanin inda kudin suka shiga.

Shin kowanne tasiri irin wadannan kiraye-kiraye ke dashi ga manyan hukumomi da kamfanonin Man-Fetur a Najeriya? A hirarsa da Muryar Amurka, Kabir Dakata, babban Daraktan Cibiyar Wayar da kan al'umma akan shugabanci nagari da kuma tabbatar da adalci wato KAJA ya ce; "

Wannan kira da SERAP ta yi abu ne mai muhimmanci kuma ya zama tilas kamfanin NNPCL ya fito ya bayyana adadin gangar man da kamfanin ke haka a duk rana, tun kafin azo matsayi irin na SERAP, ganin cewa kasafin kudin kasar ya dogara ne da ribar da ake samu a bangaren na albarkatun man-fetur. Idan kuma kamfanin NNPCL yayi burus game da wannan kira na SERAP, to yan kasa suna da yanci daukar mataki da doka ta tanadar akan kamfanin NNPCL."

Yanzu dai 'yan kasar sun fara shakkun yadda kudaden cire tallafin man-fetur zai saukaka musu rayuwa.

Saurari rahoton Rukaiya Basha:

Your browser doesn’t support HTML5

Ƙungiyar SERAP Ta Buƙaci Kamfanin NNPCL Ya Fito Da Bayanan Adadin Gangar Ɗanyen Man Da Yake Haƙa A Duk Rana