Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Maka Shugaba Buhari A Kotu Saboda Bacewar Naira Biliyan 3.8


Shugaba Buhari, SERAP
Shugaba Buhari, SERAP

Kungiyar nan ta tabbatar da adalci da kare hakkin bil'adama – SERAP, ta kai karar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, bisa zargin kin gudanar da bincike akan kudaden sha’anin kiwon lafiya kusan naira biliyan hudu da ake zargin sun yi batan dabo.

SERAP ta yi da’awar cewa an kebe kudaden ne domin ma’aikatar lafiya ta tarayya, da asibitocin koyarwa, cibiyoyin kiwon lafiya da kuma hukumar kula da ingancin abinci da magunguna, NAFDAC.

Kungiyar ta ce wannan na kunshe a cikin rahoton binciken kudi da ofishin babban mai binciken kudade na tarayya ya fitar a shekara ta 2018.

Shigar da karar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce akan balaguron da shugaban kasar yayi zuwa birnin London domin duba lafiyarsa, a yayin da kuma likitocin kasar ke cikin yajin aiki akan kin biyansu albashi da wasu hakkoki da suka shafi hatsarin yaki da annobar COVID-19.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

A cikin takardar gabatar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/433/2021 da aka shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, kungiyar ta SERAP na neman kotu da ta tilastawa Shugaba Buhari gudanar da bincike akan kudin da adadinsu ya kai naira biliyan 3.8 na sha’anin kiwon lafiya.

Haka kuma kungiyar na bukatar umartar shugaban kasa da ya gudanar da bincike akan dimbin zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka mamaye ma’aikatar lafiya ta tarayya, da asibitocin koyarwa da kuma hukumar NAFDAC.

A cikin karar, kungiyar ta bayyana cewa “cin hanci da rashawa a bangaren kiwon lafiya ya kara fadada rashin raba-daidai a bangarori da dama na rayuwa, da suka hada da tattalin arziki, siyasa, muhalli da sauransu, inda kuma ya sa ayukan kiwon lafiya sai masu hannu da shuni, da kuma manyan ‘yan siyasa.”

Shugabannin SERAP
Shugabannin SERAP

Kungiyar ta SERAP ta kara da cewa “rashin bincikar makomar kudaden da suka bata na sha’anin kiwon lafiya da kuma hukunta duk wadanda aka kama da aikata laifi, ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin hatsari da mawuyacin hali ta fuskar kiwon lafiya, wanda hakan kuma ya kai ga sabawa dokokin kare hakkin bil adama na kundin tsarin mulkin kasa, da ma na kasa-da-kasa.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG