Kungiyar sa ido ta ONET ta yaba da yanayin kwanciyar hankali lokacin zaben Nijar

Kasar Nijar

A yayin wani taro manema labarai da tayi a cibiyar kungiyar NPCR ta Nuhu Muhammadu Arzika kungiyar sa ido da ake kira ONET ta yaba da yanayin kwanciyar hankalin da aka gudanar da zaben Jamhuriyar Nijar

Duk da kwanciyar hankalin da kungiyar ta yaba tace bayanan da ta tattaro daga sassa daban daban na kasar sun nuna cewa zaben na ranar ishirin da daya da kuma ishirin da biyu na wannan watan ya sha fama da cikas sanadiyar rashin inganracen tsari.

Alhaji Mustapha Kadi Umani na cikin shugabannin kungiyar ta ONET ya yi misali da jihar Tawa a wurin da aka bude rumfunan zabe 817 amma ajihar Agadez rumfuna shida aka bude kafin lokaccin zaben lamarin da ya sabawa dokar kasar.

Saidai tun a washe garin zaben wasu kungiyoyin kasa da kasa na sa ido suka yaba da zaben a wani bayanin wucin gadi. Sai dai ita kungiyar ONET ta ce kungiyoyin kasa da kasa daga otel dinsu ne suke rubuta rahotanninsu ba su dake da wakilai koina a kasar ba. Dalili kenan da rahotanninsu ba zasu zo daya ba.

Kungiyar ONET ta hakikance an yi kazamin zabe. An yi magudi tare da barin yara su jefa kuri'a. A wasu wuraren kwacen kuri'u aka yi tare da sata. Kungiyar tace tana da shaidu da ganao da dama.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar sa ido ta ONET ta yaba da yanayin kwanciyar hankali lokacin zaben Nijar - 2' 55"