Kungiyar Red Cross Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dubi Halin Da Jama'a Ke Ciki A Yankin Sahel

Kungiyar Red Cross ICRC

Shugaban kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross Peter Maurer ya gudanar da ziyara a jihohin Tilabery da Diffa don duba halin da jama’a ke ciki a wadanan yankuna masu fama da matsalolin tsaro  da illolin canjin yanayi.

A taron manema labaran da ya kira shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ya sanar cewa bayan ganawa da hukumomin Nijer wannan rangadi ya ba shi damar sanin zahirin girman matsalar tsaron da ake fama da ita musamman a yankunan Diffa da Tilabery da Arewacin kasar.

A bayaninsa, Peter Maurer ya kara da cewa batun baiwa al’umma’a kariya na daga cikin ayyukan da suka dauki hankalinmu.

“Mun kuma tantauna hanyoyi hada mutane da ‘yan uwansu da batun mayar da ‘yan gudun hijirar cikin gida zuwa matsugunansu na asali ga wadanda ke fatan samun tallafi domin komawa kan aiyukansu na yau da kullum.”

“A nan Nijer Kungiyar CICR na da wani babban Shirin farfado da fannin tattalin arziki da na rayuwar jama’a bada tallafin a fannin kiwon lafiya ruwan sha sannan yanayin karancin abincin da ake ciki shi ma abu ne da muke dauka da mahimmanci saboda haka ne mu shafe lokaci mai tsawo muna tantaunawa akansa a tsawon makon nan.”

Peter Maurer ya ci gaba da cewa karfafa guiwa ga mutanen da ke da nakasa domin basu damar tsayuwa da kansu na daga cikin aiyukan da suka sa gaba a yanzu haka a dukkan jihohin kasar nan kuma abinda suka gani a cibiyar nakasassu da ke Agadez a yayin ziyararsu ta jiya na nuna alamun samun nasarori.

“A kowace Red Cross ko CICR kan ware million 150 na dallar Amurka domin ayyukan agaji a Kasashen Sahel yankin dake matsayin na 3 a duniya wajen samun tallafin wannan kungiya bayan Afganisthan da Syria” a cewar shugabanta.

Yana mai cewa zasu gabatar da bukatun jama’ar wannan yanki a taron kasashen tarayyar turai da na nahiyar Afrika da zai gudana a nan gaba domin neman gudunmowar kasashen dake da hannu da shuni..

Rashin samun cikakkiyar damar isar da tallafi wajen mutanen dake cikin halin bukata a yankunan da ake fama da tashe tsahen hankula na daga cikin matsalolin da jami’an agaji ke fuskanta a yanzu haka.

Shugaban reshen kungiyar a nan Nijer Francois Morellon yace zasu ci gaba da tuntubar dakarun gwamnati da na kungiyoyin tada kayar baya ta yadda za su samu sukunin gudanar da aiki ba tare da wata fargaba ba.

Saurari cikaken rahoton a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Red Cross Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dubi Halin Da Jama'a Ke Ciki A Yankin Sahel