YAOUNDÉ, CAMEROON - Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin Afirka Ta Tsakiya (CEMAC) ta yanke shawarar amfani da sabbin takardun kudin CFA daga ranar 15 ga watan Disamba mai zuwa. An cimma jituwa yayin wani babban taron Kwamitin Ministocin Yankin Afirka Ta Tsakiya UMAC a ranar 7 ga watan Nuwamba.
A karshen wannan shekarar kenan za a fara amfani da sabbin takardun kudaden a kasashe shida na yankin da suka hada da Kamaru, Kwango, Chadi, Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Gabon da kuma Équatorial Guinea
Don haka wannan sabon fasalin kudin da aka kammala shi a shekar 2020 zai maye gurbin kudin 2002 wanda aka yi amfani da shi a cikin yankin kusan shekaru ashirin.
Da muka nemi karin bayani kan wannan sauyin fasalin kudi daga masana tattalin arziki, Dr. Dalvarice Ngoudjou, ya ce “abin fahimta anan shi ne, sauyin samfurorin kudi wata hikima ce ta kiyaye yawan kudin jabu cikin kasa. Da kuma kawo sauƙi wajen samun canji. Wannan sauyin fasalin kuɗin zai taimaka wajen ƙarfafa kulawa da kuma dan kwalliya da ake yi wa kuɗin. Amma yin haka ba zai canza komai a harkar cinikayyar mutane ko ƙasashe ba. Ba kuma wata daraja ta musamman zata ƙara wa wannan sabon kuɗin ba”.
Dr. Edmond Kuate, shi ma yayi mana tsokacin kan yadda shi ya fahimci wannan labari. Y ce “mafi yawancin lokaci, bankuna na sauya fasalin kudi yayin da suka kula cewa kudin da aka buga ya yi karanci ko yawa da wanda ke dawowa cikin bankunan. Misali za ka ga mutane da dama suna ajiye maƙudan kudade a gidajensu maimakon su kai ajiya banki. Sauya fasalin kuɗin zai sa su fito da kuɗade da suke boye da su. Domin banki ya sanya wa'adin karban su. Ma’ana wata uku bayan an fara amfani da sabbin samfurori, amma idan lokaci ya wuce kuma, sai dai masu kudade su zauna da takardun da basu da wata daraja”.
Wani bambanci tsakanin sabbin kudaden da wadancan da za a sauya shi ne wannan karo na farko ne, inda aka bayyana duk harsunan hukuma da ke aiki a yankin CEMAC akan waɗannan sabbin rukunonin takardun kudin. Waɗannan harsunan sun haɗa da Faransanci, Ingilishi, Larabci (Chadi) da Sipaniya (Equatorial Guinea).
Saurari cikakken rahoton daga Mohamed Bachir Ladan
Your browser doesn’t support HTML5