Kungiyar Oxfam Tana Kira ga Tarayyar Turai da Kara Agaji Kan Cutar Ebola

Adam Smith na kungiyar Oxfam reshen Amurka.

Shugaban kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Ingilan, Dr. Mark Goldring, ne yayi wannan kira tareda yin gargadi kan illar rashin kara daukan matakai kan cutar.

Kungiyar agaji ta kasa da kasa da ake kira Oxfam tana kira ga ministocin harkokin waje na tarayyar turai su kara bada gudumawa a domin yaki da cutar Ebola,cutar da Oxfam tace tana iya zama mummunar bala’in da zata addabi jama’a a wannan zamani..

Shugaban kungiyar bada agaji ta kasar Ingila Mark Goldring, yayi kira da a tura Karin sojoji da kudi da jami’an kiwon lafiya zuwa kasashen saliyo da Guinea da Laberiya, kasashen da cutar tafi barna. Goldring yace kasashen da suka kasa bada tallafi domin yaki d a cutar Ebola, suna kasar taimakawa hasarar rayuka.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya tace fiyeda mutane dubu hudu da dari biyar ne cutar ta kashe a yammacin Afirka. Kawararru a fannin kiwon lafiya suna hasashen cewa Karin wasu dubban mutane ne zasu mutu saboda cutar kamin karshen wannan shekara.