IMO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne bayyan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ta ayyana dokar zaman gida a Jihar ta Imo da ma yankin baki daya, don bada hadin kai ga shugabanta Mazi Nnamdi Kanu wanda ya sake bayyana a kotu jiya.
Amma duk da hakan, wasu kungiyoyi da wasu mutane sun fito tarbar shugaban kasar, ciki har da kungiyar kare muradun kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo.
Dakta Alex Ogbonnia da ke kakakin kungiyar Ohanaeze Ndigbo ya ce sun zo Jihar Imo a wannan zuwan na shugaba Buhari ne don wasu dalilai biyu.
Ya ce, “Daya daga cikin dabi’un gargajiya na kabilar Igbo shi ne idan mutum ya zo gurinka ka yi mishi marhaban, a kowane irin halin da ku ke da shi. Na biyu kuma shi ne muna ganin wannan ziyarar ta shugaba Buhari Imo wata dama ce ta tunatar da shi cewa har yanzu ‘yan kabilar Igbo na bukatar sakin Nnamdi Kanu. Kuma za mu sake mika masa wannan sakon.”
Sai dai wani mai fashin baki kan lamuran siyasa, Mista Onwuasoanya Jones, na ganin wannan ziyarar baza ta yi wani tasiri ba. Inji shi, “Wannan biki ne kawai na siyasa wanda bai da wani amfani ga al’umma da kuma tattalin arzikin jihar Imo.
Ya kamata a ce an dauki kudin da aka kashe wajen shirya wannan ziyarar a magance wasu muhimman batutuwan da ke damun jihar a maimakon wannan ziyarar, da gwamnatin tarayya ta fi mayar da hankali kan inganta tsaro, da kuma ganin Jihar Imo ta samu tallafi don bunkasa karkara.”
Haka shi ma Casmir Osuoha ya ce bai ga amfanin ziyarar Buhari jihar ba.
Ya ce, “Zuwa don kaddamar da hanyar da an yi rabi aka bar rabi bai da amfani. Idan ka dubi hanyar Owerri zuwa Okigwe zaka ga cewa aikin ya tsaya ne a garin Anara, kuma tazara daga garin Anara zuwa Okigwe ta fi tazara daga Anara zuwa Owerri. Amma wai an kammala aiki an kaddamar. Ya ce shi dai bai ga wani amfanin zuwan shugaban kasa ba.”
Amma Mista Chisom Igboko na ganin wannan ziyarar zata kara karfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin Jihar Imo da gwamnatin tarayya, kuma ya bukaci gwamnan Jihar Imo Sanata Hope Uzodinma ya yi amfani da damar shigan fadar gwamnati ya inganta tsaro a Jihar.
Yanzu sau biyu kenan shugaba Buhari ya kai ziyara Jihar Imo, kuma a wannan karon, ya sake kaddamar da wasu ayyuka ciki har da hanyar Owerri zuwa Okigwe, da hanyar Owerri zuwa Orlu, da kuma rukunin gine ginen majalisar dokokin Jihar.
Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe:
Your browser doesn’t support HTML5