Bayan shiga tsakanin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi ta bangaren Hukumar Kula da Dokokin man fetur, da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, kungiyar masu motocin dakon man fetur ta kasar wato NARTO, ta dakatar da yajin aikin gamagari da ta shirya daga jiya litinin 19 ga watan Fabrairun shekarar 2024 da muke ciki.
Wannan matakin dai ya biyo bayan ganawar da kungiyar da wasu masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur suka fara daga jiya Litinin ya zuwa maraicen yau Talata.
Mambobin kungiyar NARTO dai sun dakatar da ayyukansu na jigilar man fetur a fadin kasar sakamakon tsadar man dizal da kuma matsin tattalin arziki a kasar.
Mambobin kungiyar NARTO sun yi barazanar tsayar da ayyukan su cir a fadin kasar tun daga jiya Litinin saboda tsadar man dizal wanda ake amfani da shi wajen jigilar man fetur da motocinsu a fadin Najeriya.
Kamar man fetur wanda a yanzu ake sayar da shi daga kan Naira dari 6 zuwa 7 kan kowace lita, farashin man dizal ya yi tashin gwauron zabi a musamman a baya-bayan nan, lamarin da ba ya rasa nasaba da tashin farashin dala a kasuwannin bayan fagge da na hukuma a kasar.
A yanzu dai ana sayar da man dizal sama da Naira dubu 1 da 250 akan kowace lita a Najeriya.
A saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5