Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mizanin Rashin Aikin Yi A Najeriya Ya Karu Da Kaso 0.8 Cikin 100 A Zango Na Uku Na Shekarar 2023


Hukumar ƙididdigar Najeriya ta NBS
Hukumar ƙididdigar Najeriya ta NBS

Hukumar Kididdiga ta Najeriya, NBS, ta bayyana cewar, an samu gagarumar karuwa a mizanin rashin aikin yi a Najeriya a zango na 3 na shekarar 2023.

A rahoton wani bincike data gudanar game da yawan ma’aikatan Najeriya a zango na 3 na shekarar 2023 wanda aka wallafa a litinin din da ta gabata, hukumar NBS ta bayyana cewar mizanin rashin aikin yi a Najeriya yayi tashin gwauron zabo daga kaso 4.2 cikin 100 a zango na 2 na shekarar 2023 zuwa kaso 5.0 cikin 100 a zango na 3 na shekarar.

A cewar NBS an samu ragowar ma’aikatan da suka shiga cikin bincike tsakanin mutanen dake da shekarun yin aiki daga kaso 80.4 cikin 100 a zango na zuwa kaso 79. 5 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023.

A sharhin da tayi game da kididdigar, NBS tace, mizanin auna yawan masu aikin yi da adadin yawan al’umma ya kasance akan kaso 75.6 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023 inda ya ragu da kaso 1.5% idan aka kwatanta shi dana zango na 2 na wannan shekarar.

“Gamayyar mizanin rashin aikin yi da na karancin guraben aikin yi dake da nasaba da lokaci a matsayin wani kaso na adadin masu aikin yin dake cikin al’umma (lu2) ya karu da kaso 17.3 cikin 100 a zango na 3 na shekarar daga kaso 15.5 cikin 100 na yadda yake a zango na 2 na shekarar.

“Kimanin kaso 87.3 na ma’aikatan da aka gudanar da kididdigar akansu a zango na 3 na shekarar 2023 masu sana’ar kansu ne.

“Kason ma’aikatan dake aikin albashi a zango na 3 na shekarar 2023 ya kai kaso 12.7 cikin 100.

Mizanin rashin aikin yin yayi gagarumar karuwa a zango na 3 na shekarar 2023 da kaso 5 cikin 100. An samu karuwar kaso 0.8 cikin 100 daga yadda yake a zango na 2 na shekarar ta 2023.

“Mizanin rashin aikin yin tsakanin mutanen da suka kammala karatun sakandare ya kai kaso 7.8 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023.”

A cewar Hukumar Kididdigar Najeriya ta NBS, mizanin rashin aikin yi tsakanin matasan dake tsakanin shekara 15 zuwa 24 ya kai kaso 8.6 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023, inda aka samu karuwar kaso 1.4 cikin 100 akan yadda al’amarin yake a zango na 2 na shekarar.

Mizanin rashin aikin yin a birane ya kai kaso 6.0 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023, inda aka samu ‘yar karuwa da kaso 0.1 cikin 100 akan yadda yake a zango na 2 na shekarar.

Kididdigar karancin guraben aikin me nasaba da lokaci ta kasance akan kaso 12.3 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023, inda aka samu ‘yar karuwa da kaso 0.5 cikin 100 yadda yake a zango na 2 na shekarar. hakan na nuni da samun karuwar kaso 1.4 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda yake a zangon na 4 na shekarar 2022.

“Kaso 4.1 cikin 100 na wadanda ke tsakanin shekarun yin aiki duk a harkar noman ci da karfi suke a zango na 3 na shekarar 2023.

Kididdigar mutanen dake aikin da ba na hukuma ba a zango na 3 na shekarar 2023 ya kai kaso 92.3 cikin, yayin da a zango na 3 na shekarar ya kasance akan kaso 92.7 cikin 100.

Rahoton ya kara da cewar, adadin matasan da basa aiki ko karatu ko koyon wata sana’a (neet rate) a zango na 3 na shekarar 2023 ya kai kaso 13.7 cikin 100.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG