Kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya NANPF, ta umarci manyan kungiyoyin kwallon kafar kasar da su biya bashin duk kudaden da yan wasa da koch Koch ke binsu.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar tace, a sakamakon rashin bin umarnin shawarar da hukumar kwallo ta NFF da kamfanin kula da kungiyoyin wasa na Najeriya suka yanke.
Hakan yasa kungiyar ‘yan wasan ta Najeriya, ta baiwa kungiyoyin da ake bi bashi kwana 14 domin su biya ‘yan wasansu, ko kuma su fuskanci abinda da zai biyo baya.
NANPF ta fara wata tattaunawa da kungiyar kwadago mai suna TUC ta Najeriya, bayan gazawar da sukayi na kakaba ma kungiyoyin takunkumi, saboda rasahn bin umarnin hukumar NFF. Kungiyar kuma ta yabawa gwamnatin jihar Kwara na biyan bashin da ‘yan wasansu sukayi, da kuma bin umarnin hukumar kwallo da sukayi.