Kungiyar Muryar Talaka a Yobe Zata Wayar da Kan Matasa

Gwamna Geidam na Jihar Yobe yana gaida wani da ya samu rauni lokacin wani hari.

Ganin yadda zabe da kyamfe ke kusantowa, kungiyar zata nemi wayarwa da mayasa kai domin su gu8je wa ayyukan bangar siyasa
Ganin yadda kakar kyame da zabubbuka ke kara kusantowa, kngiyar Muryar Talaka tana shirin fara gudanar da ayyukan wayar da kan matasa a cikin Jihar Yobe, ta yadda zasu iya kaucewa shiga ayyukan bangar siyasa.

Shugaban kungiyar a Jihar Yobe, Alhaji Sake Bagus, ya fadawa wakiliyar Muryar Amurka, Sa'adatu Mohammed Fawu, cewa kungiyar ta fara shiga lungu-lungu na Yobe domin janyo hankulan matasa su nesanta kawunansu daga bangar siyasa wadda ba zata haifar musu da wani abin alkhairi ba.

Alhaji Sale Bagus ya yaba da dangantakarsu da gwamnatin Jihar Yobe, har ma yace kungiyar tasu ta kan bi sawu domin tabbatar da cewa kayayyakin sana'ar hannu da gwamnatin Alhaji Ibrahim Geidam ke ba matasa ta hannun ma'aikatar Matasa da Raya Kasa, su na shiga hannun matasan na zahiri.

Ga cikakken rahoton wakiliyar tamu daga Damaturu.

Your browser doesn’t support HTML5

Muryar Talaka A Jihar Yobe Tana Wayarwa Da Matasa Kai - 3:52