Wani kwararre kan sha'anin tsaro, kuma tsohon jami'in tsaro na farar kaya a Najeriya, Mr. Habu Dan Mallam, ya yaba da sakin mutanen yana mai cewa tun farko abinda ya kamata ayi ke nan. Yace a kasa kamar Najeriya mai ikirarin dimokuradiyya, tilas ne a gabatar da mutum a gaban kotu idan akwai hujjar tsare shi domin kotu ta yanke hukumci kan a sake ko a tsare shi, amma ba a yi ta tsare da shi na tsawon lokaci ba tare da wata tuhuma ba.
Shi ma masanin shari'a, Barrister Solomon Dalung, ya ce sakin mutanen mataki ne mai kyau, amma ya tambayi ko wace hujja ake da ita ta kin sakin wadannan mutane tun tuni? Yace akwai kamshin siyasa a cikin lamarin, amma dai wannan matakin farko ne mai alkhairi.
Shi ma shugaban kungiyar Izala ta Najeriya, Sheikh Bala Lau, ya yaba da sakin mutanen, amma yace cin zarafi ne yadda ake kame mutanen da ba su san baki ba, balle fari, har yayi misali da wani sanannen malami na addinin Islama a Jos, Malam Nazifi, wanda aka kama ana kuma tsare da shi ba tare da an gabatar da shi a kotu ba.
Sheikh Bala Lau yayi kiran da a gaggauta sakin Sheikh Nazifi da ire-irensa wadanda naka musu yarfe, ko kuma an san cewa akwai wata makarkashiya a game da kama su da aka yi.