Bam din da ya tashi daga cikin wata mota ya faru ne wajen 1.30 na rana a cibiyar kasuwanci dake kasuwar GSM kusa da ofishin gidan telebijan din jihar da kuma gidan waya na Maiduguri.
Kawo yanzu dai babu wata manufa takamaimai ban da mutane dake saye da sayarwa a ranar Muludin Annabi Mohammed (S.W.A.). Ganau da kafofin labaran duniya da na cikin gida suka zanta dasu sun ce akalla an kai gawarwaki 40 dakin ajiye gawa a asibiti. Kana wasu mutane 50 sun jikata kuma motoci da dama da shaguna suka kone mururus. Wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da na bakin hanya da masu saye da sayarwa da iyaye da ‘ya’yansu da matuka motoci da dansanda mai ba motoci hanya.
In ji Corinne Dufka babar jami’a mai bincike kan Afirka ta Human Rights Watch ta ce “wannan aika aikar wata misali ne na yadda ake shirya kashe mutanen kasar” Ta ce “Babu wani dalilin kai hari kan mutanen da suke neman samun abun rayuwar yau da kullum”
Yayin da dakarun tsaro zasu kai martani su yi hakan tare da mutunta ‘yancin duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin.
Harin baya bayan nan yana cikin jerin hare-haren da ‘yan tsageran Islaman Najeriya, wato Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati waj-Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram suka shirya. Kodayake babu wanda ya fito karara ya dauki alhakin wannan harin , kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare kan kan jama’ar arewacin Najeriya tun daga watan Yulin shekarar 2009 sabili da haka kowa ma na zaton kungiyar ce ta kai harin ranar 14 ga watan Janairu.
Kawo yanzu kidigdiga ya nuna wajen mutane 2000 a arewacin Najeriya bama bamai suka hallaka a hare-haren da aka kai kan kauyuka,da garuruwa da kwalajoji da wuraren ibada har ma da manyan hanyoyin sufuri. Boko Haram na kaddamar da mugun tashin hankali kan gwamnatin Najeriya a kokarin da ta keyi domin kafa daula mai bin tafarkin shari’ar Musulunci bisa ga nata fahimtar. Tun watan Mayun 2013 hare haren suka karu lokacin da gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta baci a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.
A watan Nuwamba lokacin wata ziyarar bincike zuwa Maiduguri da Human Rights ta yi ta bayyana yadda Boko Haram take shirya hare-hare da bayan an fatartaketa daga inda ta kafa sansani a Maiduguri. Maharan sun kashe daruruwan mutane da yin kacakaca da gawarwakin yawancinsu da kuma sace wasu da yawa musamman mata da yara mata.
Hare-haren sun ci gaba har da wanda aka kai kan masu bikin aure ranar 28 ga watan Disamban bara a kauyen Tashan Alede da kuma na wani kauyen Kwajjafa dake kusa inda aka kashe mutane 12. Cikin ‘yan watannin nan Boko Haram ta farma shaguna inda ta kwashi ganima ta konesu har da motoci kana ta yi ta yi anfani da ‘yan yara ‘yan shekaru 12 kai haere-hare.
A shekarar 2012 Human Rights Watch ta yi nazarin yadda tashin tashina suka mamaye al’ummomin arewa maso gabas da na tsakiyar arewa.
Har wau yau Human Rights Watch ta bayyana yadda dakarun tsaron Najeriya su kan wuce gona da iri a kokarin mayarda martani lamarin da ya hada da kama dimbin mutane barkatai wadanda suka hada da matasa maza daga kasuwanni da masallatai da ma wasu wuraren. Cikin shekaru hudun da kungiyar Boko Haram ta yi tana tada hankali gwamnatin Najeriya ta kasa bada cikakken bayani kan daruruwan maza da matasa da har yanzu babu labarin inda suke. Yakamata gwamnatin Najeriya ta bada bayani kan wadanda suka bace ta kuma tabbatar da cewa duk ayyukan tsaro sun bi tsarin kasa da kasa dake daidai da kare hakin dan adam.
“An san cewa jama’a zasu matsawa dakarun tsaron Najeriya su mayarda martani kan hare-haren su kuma tabbatar da tsaro ma wadanda yanzu sun firgita” inji Dufka. “Amma kuskuren yin anfani da iko ta hanayar da bai kamata ba zai kara rura wutar tashin hankali a Najeriya ne, yana kuma iya kara harzuka kungiyoyi irin su Boko Haram