Barrister Solomon Dalung daya daga cikin shugabannin kungiyar dattawan arewa ko ACF a takaice ya ce sun gayawa gwamnatin tarayya abubuwan da ake yiwa arewa kamar cin zali da cin mutunci da danniya. Ya ce kuma akwai wasu abubuwa dake da manufar son bankada ma kasar wuta.
Sabili da haka ya kira sarakunan arewa su tashi tsaye domin su ne iyayen kasa. Ya ce tun kafin bature ya zo suna mulki. Sarakuna su ceci kasar. Ya ce taronsu shi ne rigakafin damuwar arewa. Masarautun Sokoto da Borno sun yi shekaru aru-aru kuma irin rigingimun yanzu an yi lokacinsu amma ai sun warwaresu.
A bincika yaya aka yi har aka yi maganinsu.Su sarakunan ne suka yi maganinsu. Sabili da haka a koma wurin sarakuna a jawo hankalinsu su yi anfani da basirar kakanninsu su jawo hankulan mutane a magance riginmun da suka addabi arewa.
Ya ce sun gargadi sarakuna su yi takatsantsan da 'yan siyasa domin suna yawo da man fetur da ashana domin tada wutar rigima. Babu abun da 'yan siyasa ba zasu yi ba har ma satar kuri'u domin su cigaba da mulki. Ya kira sarakuna su tsaya a matsayinsu na iyaye su kwatowa arewa hakinta domin kasafin kudin bana ya nuna arewa baki daya an cuceta. A gayawa 'yan majalisa daga arewa cewa ba za'a yadda da kasafin kudin ba.
Barrister Dalung ya ce yadda sarakuna suka fito taron ya nuna cewa taro ne da ya fi karfin na shan shayi. Nadamar ma da suka yi ya sake nunawa zancen da a keyi ya fi karfin wasa. Mutanen da suka kawo labarin cutar da a ke yiwa arewa mutane ne da an sansu. Mutane ne kuma da suka fi karfin zuciyarsu. Mutane ne da shugaban kasa ba zai iya ya sayesu ba. Taron na masu hankali ne, kuma na shugabannin arewa domin su ga ina ne abun da suka gada daga wurin iyayensu ya kwana.
Abubuwan da dattawan arewa basu yadda da su ba sun hada da kin amincewa da cutar da a keyiwa arewa da kwashe manya manyan makamai daga arewa zuwa kudu da siyasar raba hankalin mutane domin a ci zabe da kuma cusa addini cikin harkokin siyasa. Dattawan sun yi tur da halin ko in kula da gwamnatin tarayya ke yi game da abubuwan dake faruwa a arewa. Idan mayya ita ce mai karban gaisuwar mutuwa to 'ya'ya zasu cigaba da mutuwa. Daga karshe arewa bata yadda da taron hada kan kasa ba. Idan kuma za'a yi taron kasa to ya zama mai cin gashin kansa, wato wadanda ke kan mulki yanzu su nade nasu-i-nasu a nada gwamnatin riko kana a yi taron kasa. To a wurin taron jama'ar kasar zasu dauki shawarar ko a cigaba da zama tare ko kowa ya kama tasa hanyar.
Ga rahoto.