Tashe-tashen hankula masu nasaba da aiyukan ta’addanci da ake fama da su a duniya ya sa taron na ministocin harkokin wajen kasashen maida hankali akan wannan al’amari da nufin bullo da hanyoyin da zasu taimaka a samo mafita.
Kungiyoyin ta’addanci kan fake da addini wajen kashe mutane ta hanyar kai munanan hare-hare a sassan duniya, alhali addinin Islama ya haramta aikata irin wannan danyen aiki, a saboda haka kungiyar OCI ke ganin ya zama wajibi ta tashi tsaye domin warware wannan kulli.
A jawabinsa na bude taron, Shugaban Nijer Issouhou Mahamadou ya ce ta’addanci shi ne babban makiyin addinin Islama kuma ta’addanci cin amanar musulunci ne. Kashi 82 daga cikin 100 na mutanen da ta’addanci ya rutsa da su Musulmi ne, wadanda galibi kasashensu ke fama da matsin tattalin arziki da na rayuwa.
La’akari da irin wadannan matsaloli ya sa majalisar ministocin harkokin wajen ta shawarci bangarorin da ke rikici a kasashen Musulmi mambobin kungyar OCI ko OIC su ajiye makamai domin samar da maslaha a tsakaninsu, matakin da ake gani zai taimaka a murkushe ayyukan ‘yan ta’adda inji shugaban majalisar ministocin, kuma ministan harkokin wajen Nijer Kalla Hankourao.
Taron ya kuma bayyana juyayi game da rasuwar tsohon shugaban kasar Nijer Tandja Mamadou.
Mai magana da yawun kasashen yankin Afrika, kuma ministar harkokin wajen kasar Senegal Aissata Fall Tall, ta ce kungiyar OIC ba za ta taba mantawa da marigayin ba, saboda yadda a shekarar 2009 ya yi kiran kasashen duniya su yafe wa kasashen musulmi bashin da ake binsu, kuma a yanzu haka kasashen na OCI na da irin wannan bukata sanadiyar koma bayan da annobar coronavirus ta haddasa.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5