Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ahmed Ya Ce Ba Zai Tattauna Da Jami'an Tigray Ba Yayin Da Yaki Ke Kara Zafi


Firai Ministam Habasha Abiy Ahmed
Firai Ministam Habasha Abiy Ahmed

Dakarun Habasha na samun nasara a garuruwa da dama a kusa da babban birnin yankin Tigray, wuni guda bayan da gwamnatin ta ce ta fara aiwatar da matakin karshe na fatattakar yankin arewacin kasar, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar a jiya Juma’a.

Laftana Janar Hassan Ibrahim ya fada a wata sanarwa a jiya Juma’a, cewa dakarun tarayyar sun kwace garin Wikro kana zasu kwace ikon Mekelle a ‘yan kwanaki masu zuwa a cewar Reuters.

Ci gaba da yakin na zuwa ne a daidai lokacin da Firai ministan Habasha Abiy Ahmed ya gana da tawagar wakilai daga Kungiyar Tarayyar Afrika da ta hada da tsohuwar shugaban Liberia Ellen Johnson Sirleaf da tsohon shugaban Mzanbique Joaquim Chissano da kuma Kgalema Motlanthe daga Afrika ta Kudu a birnin Addis Ababa, inda Ahmed ya ce tattaunawa da Tigray ba zai yiwu ba.

A sanarwar bayanan ganawar, Abiy ya yabawa kokarin kungiyar tarayyar Afrika na shiga tsakani, ya ce gwamnati ta himmantu wurin kare fararen hula amma kuma bai yi batun tattaunawa da Jami’an Tigray ba.

Kira game komawa ga teburin tattaunawa na karuwa, yayin da yakin ke kara ta’azzara zuwa makwabciyar Eritrea kana yana barazana ga zaman lafiyar yankin kuriyar Afrika.

Jami’an Tigray suna zargin sojojin Eritrea da shiga cikin yakin suna taimakawa bangaren rundunar gwamnatin Abiy a Habasha. Zargin da jami’an Eritrea suka musunta na sa hannu a wannan yaki.

XS
SM
MD
LG