Kungiyar Makiyayan Tubutul Bulago a Nijar Ta Yi Taron Wayar Da Kan Makiyaya Akan Kaucewa Tarkon Ta’addanci  

NIGER: Taron Makiyaya

Wata kungiya mai bunkasa kiwo a Nijer mai suna Tubutul Bulago ta gudanar da taron ta na kasa a garin Tahoua, inda ta ja hankalin matasa makiyaya da su kauce wa fadawa tarkon ta'addanci ko satar mutane don neman kudin fansa.

TAHOUA, NIGER - Taron dai na da nasaba da girka sabon kwamitin gudanarwa na jiha na kungiyar, bisa la’akari da cewa kiwo na a sahu na biyu bayan noma a jamhuriyar Nijer wajan bunkasa tattalin arziki.

Kungiyar ta ce ta na kokari daidai gwalgwado wajen hana ‘ya’yan makiyaya shiga ta'adanci, ko garkuwa da mutane, ko kwace wa jama'a dukiyoyin su a cewar shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Mainsara Abdu.

A nasa bangaren shugaban kungiyar na jihar Tahoua Mahammadu Usman, cewa yayi idan ana son a magance wannan matsalar to dole ne gwamnati ta tsayar da makiyaya wuri guda.

Ita ko shugaba ta mata makiyaya ta wannan kungiya Hadiza Adamu, cewa ta yi suna iya nasu kokari domin su ankarar da ‘ya’yan makiyaya akan abubuwan da suka hada da kunna wuta domin yin abinci ko hada shayi a lokacin da suke zuwa wurin kiwo da ka iya rikidewa zuwa gobarar daji.

A baya-bayan nan dai makiyaya na shan suka da ma kyama a yammacin nahiyar Afrika kamar Najeriya, bisa zarginsu da hannu a ayyukan garkuwa da mutane da ta'adanci.

Saurari rahoto cikin sauti daga Harouna Mamane Bako:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Makiyayan Tubutul Bulago a Nijer Ta Yi Taron Wayar Da Kan Makiyaya Akan Kaucewa Tarkon Ta’addanci