Taron wannan shekara na kungiyar mai kokarin kare hakkin makiyaya wato FUDECO a takaice, ya mai da hankali ne akan ilimin makiyaya da hadin kai domin magance matsalolin da ke fuskantar su ya nunar da bukatar kyautatawa makiyaya zato.
Farfesa Abubakar Abba Tahir, malamin jami'a ne kuma ya na cikin 'yan kwamitin amintattu na kungiyar makiyaya ta FUDECO, ya ce ana shafawa makiyaya kashin kaji. Ya ce kamar kowace al'uma, Fulani na kwadayin zaman lafiya, a dan haka suna ci gaba da musanta zargin da ake yiwa Fulani na aikata miyagun ayyuka.
Duk da zargin da ake yiwa Fulani ko makiyaya akan matsalolin tsaro ma ita mukaddashiyar shugaban kungiyar ta FUDECO Dr. Nafisatu Dahiru Mohammad, ta ce su ma matsalar ta hada da su. Ta ce dole a duba sosai a kan zargi da ake yiwa Fulani, saboda batun rashin zaman lafiya ya shafi kowa.
Shugaban kwamitin da ya shirya wannan taro Barista Abubakar Ibrahim Naseh, ya ce burin kungiyar shine sauya rayuwar makiyaya.
Taron kungiyar makiyayan da ya sake zaben sabbin shugabanni dai ya tashi kan cewa dole gwamnati ta rinka tafiya tare da Fulani ko makiyaya cikin dukkanin tsare-tsaren ta, da kuma ayyukan ci gaba domin magance matsalolin da ke damun Najeriya baki daya.
Ga dai rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5